Kungiyar Wikileaks tace zata ci gaba da wallafa takardun diflomasiyya na sirri na Amurka, duk da kama mutumin da ya kafa wannan kungiya, kuma babban editanta, Julian Assange, a kasar Britaniya.
A sanarwar da kungiyar ta Wikileaks ta bayar ta hanyar sadarwar Twitter a Internet, ta ce kama Assange ba zai shafi ayyukan kungiyar ba, kuma a daren yau ma za su wallafa wasu daga cikin takardun kamar yadda suka saba yi kowane dare.
Mutumin da ya kafa kungiyar Wikileaks ya mika kansa ga ‘yan sanda yau talata a London, a bayan da kasar Sweden ta bayar da takardar iznin kama shi bisa zargin yin fyade. Ya musanta wannan zargi da ake yi masa.
An shirya zai bayyana gaban kotu yau talata a London.
Wannan zargi da ake yi ma Assange ya samo asali daga ikirarin da wasu mata biyu da ya hadu da su a Sweden a watan Agusta suka yi ne, kuma bai shafi wallafa takardun diflomasiyya na sirri na Amurka da wannan kungiya take yi ba. Amma lauyansa, Mark Stephens, ya bayyana wannan zargi na fyade a zaman wata makarkashiyar siyasa.
A makon da ya shige kungiyar Wikileaks ta fara wallafa wadannan takardun diflomasiyya ta Internet da kuma wasu manyan jaridu guda biyar, watau “The Guardian” da “New York Times” da “Der Spiegel” da “Le Monde” da kuma “El Pais.” Jami’an Amurka sun ce wannan fallasar ta jefa tsaron kasa na Amurka cikin hatsari, kuma an fara gudanar da bincike na aikata babban laifi.
A cikin wani ra’ayin da ya buga a jarida mai suna “Australian” yau talata, Assange ya kare kungiyar, yana mai fadin Wikileaks tamkar kafar yada labarai ce, kuma fadin gaskiya na sa gwamnatoci su guji shirga karya.
An rufe kwamfutocin dake dauke da bayanan sirrin da Wikileaks ta wallafa a yayin da ake ci gaba da daukar karin matakan siyasa kan wannan kungiya. Amma magoya bayan Wikileaks sun bude daruruwan dandalin Internet dake dauke da kofen takardun ta yadda har yanzu ana iya shiga a gansu.