Shugaba Barack Obama na Amurka ya bada shawarar tsaida Karin albashin ma’aikatan Gwamnatin tarayya domin hakan ya taimaka wajen cike gibin miliyoyin dalolin da ake bukata da nufin kaucewa samun wani cikas wajen bunkasa tattalin arzikin Amurka. A yau litinin shugaban na Amurka ya bada wannan shawarar a wani jawabin da ya yiwa kwamatin hadin gwiwar jam’iyyu a fadar shugaban Amurka ta White House. Shugaba Obama yace cike gibin kasafi na bukatar gudummawar daga kowane bangare na Amurka. Tsaida Karin albashin ma’aikatan tarayya zai dauki tsawon shekaru biyu, ciki har da ma’aikatar tsaron Amurka, amma banda rundunar sojin Amurka. Fadar shugaban Amurka ta bada sanarwar cewa tsaida Karin albashi zai taimaka a sami ajiyar Dala miliyan dubu biyu daga cikin kasafin kudin shekarar 2011, a kuma yi ajiyar Dala miliyan dubu 28 cikin shekaru biyar har zuwa sama da Dala miliyan dubu sittin cikin shekaru goma masu zuwa. An shirya a gobe talata shugaba Barack Obama zai tattauna da shugabannin jam’iyyar Republican kan matakan da Gwamnati ke dauka don bunkasa tattalin arzikin Amurka.
Shugaba Barack Obama na Amurka ya bada shawarar tsaida Karin albashin ma’aikatan Gwamnatin tarayya
Shugaba Barack Obama na Amurka ya bada shawarar tsaida Karin albashin ma’aikatan Gwamnatin tarayya .