Ana sa ran jawaban Firai ministar Burtaniya Theresa May a taron na kwanaki biyu zai hada da ba da tabbacin makomar mutane miliyan uku na sauran kasashen tarayyar turai da a yanzu haka suke zaune a Burtaniyyan.
Haka kuma idan aka hada da zancen makomar mutane fiye da miliyan daya ‘yan Burtaniya dake zama a wasu kasashen tarayyar turai, ana iya gane cewa wannan na daya daga cikin manyan batutuwan da dole bangarorin biyu su amince da su a wannan zaman shawarwarin da aka fara farkon makon nan.
Bayan May ta yi jawabi, a daren yau Alhamis, sauran shugabannin tarayyar za su ci gaba da taron ba tare da ita ba domin tattauna nasu bangaren shirin ballewar Burtaniyyar daga tarayyar turai.
A bara ne aka jefa kuri’ar raba gardama a Burtaniya, sakamakon da ya amince da ballewar kasar daga kungiyar.
Ana sa ran za a gama shirin a watan Maris din shekarar 2019.