Kungiyar Tarayyar Turai Da Japan Sun Sa Hannu A Wata Yarjejeniya

A wani yunkuri na kara farfado da harkokin kasuwanci da tattalin arziki, kungiyar tarayyar Turai da kasar Japan sun rattaba hannu akan wata yarjejeniyar cinikayya.

Kungiyar tarayyar turai da kasar Japan sun sa hannu a wata sabuwar yarjejeniyar cinikayya yau talata a Tokyo, wadda shugaban kungiyar tarayyar turai Donald Dusk ya kira haske a cikin duhu dake karuwa a siyasar kasashen ketare.

Sabuwar yarjejeniyar cinikayyar zata cire kashi casa'in da tara cikin dari na jaddawalin kudin fito a kayyayakin Japan zuwa ga kasashen tarayyar turai wadanda suka hada da motoci, kayyayakin lantarki da kuma amfanin gona daga kasashen tarayyar turai zuwa Japan, wadanda suka hada da man shanu, ruwan inabi, da naman alade. Za'a kuma samu saukin shigar da sinadarai daga tarayyar turai zuwa Japan.

Tusk tare da shugaban kwamitin tarayyar turai Jean-Claude Junker sun hadu da firayin ministan Japan Shinzo Abe don yima manema labarai jawabi bayan sa hannu a yarjejeniyar.