Kungiyar Tarayyar Afirka (AU) ta Kori Guinea-Bissau

Dan takarar Shugaban kasa na jamiyya mai mulkin Guinea-Bissau Carlos Gomes Junior ke jawabi ga magoya bayansa

Tarayyar Afirka ta bada sanarwar jingine wakilcin kasar Guinea-Bissau

Tarayyar Afirka ta bada sanarwar jingine wakilcin kasar Guinea-Bissau a dalilin juyin mulkin da soja suka yi.

Yau Talata kwamatin ayyukan kare zaman lafiya da harkokin tsaro na tarayyar Afirka yayi zama na musamman kan kasar Guinea-Bissau wanda bayan zaman taron majalisar kokin tayarra Afirka ta bada sanarwar dakatar da wakilcin kasar Guinea-Bissau har sai lokacin da kasar ta koma ga bin tafarkin salon mulkin Demokuradiyya.

Sanarwar dake dauke da sa hannun shugaban tarayyar Afirka Jean Ping tayi watsi da wani yunkurin da shugabannin mulkin sojin kasar Guinea-Bissau keyi na yin jurwayen kafa majalisar maida mulkin ga farar hula. Yace tun farko me ya janyo kuyin mulkin?

Kuma sojin da suka yi jagorancin juyin mulkin sun sani sarai suna yin watsi da abinda kundin tsarin mulkin kasar ya tanadar, don haka yayi kira ga ‘yan siyasar kasar Guinea-Bissau da su kauda jiki daga karbar duk wani mukamin daga wajen shugabannin sojin da suka yi juyin mulki.