Shedu gani da ido sunce sojojin sun mamaye titunan Bissau baban birnin kasar Guinea Bissau a yayinda suka kaiwa gidan Prime Minista wanda kuma dan takarar shugaba ne wanda yafi kowa samun kuri'u Carlos Gomes hari.
Ba'a dai san inda shi wannan dan siyasa yake bayan da ba'a tabbatar da rikicin data auku a kasar a jiya Alhamis ba.
Tuni dai kungiyar Habaka tattali arzikin kasashen Afrika ta yamma da ake cewa ECOWAS a takaice ta bada sanarwar yin Allah wadai da yunkurin juyin mulki.
Shedun gani da ido sunce sojoji sun kama 'yan siyasa, sa'anan suka mamaye hedikwatar jam'iyar dake jan ragamar mulkin kasar da gidan rediyon kasar a yayinda aka ji karajin harbe harbe dana rokokin da aka harba a baban birnin kasar,
Ofishin jakadancin Amirka a birnin Dakar kasar Senegal, wanda shine ke kula da muradun Amirka a kasar Guinea Bissau ya aikawa Amerikawa da suke zaune a kasar sakon, akan cewa gaggawa ,su guji zuwa cikin garin birnin Bissau. Ofishin yace tana yiwuwa tarzoma a birnin kila anyi juyin mulkin ne ko kuma anyi yunkurin yi
Wannan al'amari dai ya faru ne a jajibirin fara yakin neman zaben fidda gwamni da za'a yi. Masu hamaiya a kasar karkashin jagorancin dan takarar daya zo na biyu, Kumba Yalla sun bukaci a kauracewa zaben fidda gwani da aka shirya yi a ranar ashirin da tara ga wannan wata na Afrilu idan Allah ya kaimu. Kumba Yala yana daga ciki yan takarar shugaban kasa guda biyar da yayi ikirari cewa an tupka magudi a zagaye na farko na zaben da aka ti.