Kungiyar Taliban Tayi Alkawarin Ci Gaba Da Kai Hare Hare Kan Amurka

Afghan Taliban

Afghan Taliban

Kungiyar Taliban taci alwashin zafafa hare hare kan cibiyoyin Amurka, tana Allah wadai da shawarar da Amurka ta yanke na jinkirta janye dakarunta daga Afghanistan.

Mayakan kishin Islaman sun maida martani ne ga sanarwar da shugaba Barack Obama ya yi cewa, zai bar dakarun Amurka dubu tara da dari takwas dake Afghanistan a halin yanzu, har zuwa karshen shekara ta dubu biyu da goma sha shida, kafin rage yawansu zuwa dubu biyar da dari biyar zuwa lokacin da zai bar mulki a watan Janairu shekara ta dubu biyu da goma sha bakwai.

Tun farko gwamnatin shugaba Obama tayi shirin barin sojojin Amurka dubu daya ne kawai bayan shekara ta dubu biyu da goma sha shida, tare da maida hankali kan tsaron ofishin jakadancin Amurka a Kabul.

A wata sanarwa da kakakin kungiyar Taliban Zabihullah Mujahid ya turawa muryar Amurka ta email yace, kungiyar mayakan tasha jaddada cewa, dakarun Amurka ba zasu daina mamayar da suke yi a Afghanistan ba, kuma suna alkawuran da basu da niyar cikawa da nufin yaudarar ‘yan Afghanistan da kuma Amurkawa ne kawai.

Sai dai wani dan majalisar dokokin Afghanistan Shukria Barikzai yace tura lokacin janye dakarun zuwa gaba ya yi dace.

Shugaban kasar Afghanistan Asharaf Ghani shima ya yi na’am da wannan shawarar, yace ta kara bayyana irin dangantaka ta kut da kut dake tsakanin Amurka da Afghanistan.