Kungiyar Super Eagle Ta Shirya Don Shiga Gasar Kofin Afrika

A shirye shiryen da Kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles dake tarayyan Najeriya, sukeyi na fuskantar wasan neman tikitin shiga gasar cin kofin nahiyar Afrika, na shekara 2019 wadda zai gudanar a kasar Kamaru.

Rahotanni na nuni da cewa tuni 'yanwasan Najeriya su 21 wanda suka hada da Ahmed Musa da wasu 'yanwasa da suka hada da Isa Uyo, babban birnin jihar Akwa Ibom kafin ranar Asabar a wasan da za suyi a kasar Libya.

Ku Duba Wannan Ma Kaftin John Terry Na Shirin Ajiye Takalmi, Zai Yi Murabus

'Yanwasan da suka samu halartar sansanin horaswar sun hada da masu tsaron raga Francis Uzoho, Ikechukwu Ezenwa, Daniel Akpeyi, sauran 'yanwasan sune William Troost-Ekong, Semi Ajayi, Leon Balogun, Olaoluwa Aina, Jamilu Collins, Abdullahi Shehu, Chidozie Awaziem, Kenneth Omeruo, Wilfred Ndidi, Samuel Kalu, Ogenyi Onazi, John Ogu, Oghenekaro
Etebo, akwai 'yanwasan gaba kamar, Isaac Success, Alex Iwobi, Moses Simon, Henry Onyekuru, da kuma Kelechi Iheanacho.

A yau ake sa tsammanin isowar Bryan Idowu, da kuma danwasan gaba Odion Ighalo, Alkalan wasan da za suyi al'kalanci sun fito daga kasashe daban daban wanda ya hada da kasar Jamhuriyar Congo, kasar
Mali, Afrika ta kudu, inda ake sa ran isowarsu Najeriya gobe Jumma'a a
da safe.

Your browser doesn’t support HTML5

Kungiyar Super Eagle Ta Shirya Don Shiga Gasar Kofin Afrika 3'20"