Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Alamu Sun Nuna Cewar Za'a Iya Sallamar Jose Mourinho


Tsohon dan wasan tsakiya na kungiyar Manchester United wadda yanzu yake horas da tawagar Kungiyar kwallon kafa na kasar Wales dake Birtaniya, maisuna Ryan Giggs, ya roki mahukunta a kungiyar da su kara hakuri kada su sallami mai horar da 'yanwasan kulob din Jose Mourinho.

A cewar Giggs duk da Manchester United na fuskantar kalubale a halin yanzu, ya bayyana kwarin gwiwarsa kan cewa lamarin zai sauya, kuma nasara zata sake zuwa kungiyar.

Kocin Mourinho, na fuskantar suka daga ciki da wajen kungiyar ta United, wadda ya hada da magoya bayanta, ganin yadda ya jagoranci wasanni hudu, ba tare da samun nasara ba a gefe guda.

A yayin da yake fuskantar rashin jituwa tsakaninsa da danwasan tsakiyar kulob din Paul Pogba, dan wasan da yafi kowa tsada a kungiyar.

A baya bayan nan dai wasu masu fashin baki kan harkar wasanni, sun furta ra'ayin su na cewa, zai yi wahala a ce kungiyar ta United bata sallami Mourinho ba, mutane da dama na zaton cewa kila tsohon mai horar da Real Madrid Zinaden Zidane ne zai maye gurbinsa.

Inda wasu jaridu suka wallafa cewa Zidane yanzu haka yana koyan iya magana da harshen turanci domin komawarsa Manchester United a kasar Ingila.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:49 0:00

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG