Kungiyar ISIS Ta Kashe Kiristoci 30 'Yan Kasar Habasha dake Aiki a Libya

Mayakan ISIL Suna yiwa mutane kisan gilla.

Fadar White House tayi tur da kisan gilla da kungiyar ISIS ta yiwa wasu kiristoci 30 'yan asalin kasar Habasha

Fadar White House ta nan Amurka tayi suka da kakkausar lafazi sabili da kashe wasu Kiristoci ‘yan kasar Habasha su 30 a kasar Libya da ‘yan kungiyar ISIS suka aikata.

Mai magana da yawun fadar ce tayi wannan kalami jiya Lahadi tace an kashe wadannan mutanen ne kawai domin addininsu daban yake da na ‘yan kungiyar taISIS. Tace lamarin ya nunaa sarari cewa yan kungiyar ISIS tunanensu baya da banbanci dana dabbobi,

Tace wannan kissan ya nuna a fili cewa akwai bukatar kasar ta Libya ta gaggauta shawo kan matsalar siyasar kasar dominhada kai a yaki yanta’addan dake damun kasar.

Domin nuna cewa sune suka aikata wannan danyen aikin,

Kungiyar ta ISIS ta nuna a wani faifan bidio inda wasu mutane ke durkushe a bakin teku inda aka fille musu kai kana wasu kuma aka harbesu a wuya da bindiga.

A wani kisa mai kama da irin wannan an nuna a cikin faifan bidio a cikin watan Fabarairu inda aka nuno yan kungiyar ta ISIS suna sare kan wasu mabiya addinin kirista yan asalin kasar Masar.

Kungiyar kasashen Larabawa ta shaidawa kanfanin dillanci labarai na Faransa cewa manyan shugaban hafsoshin sojan kasashen zasu gudanar da taro a Cairo domin tattauna yadda zasu tinkari wadannan yan ta’addanda suka addabi yankin nasu.