Kungiyar Philadelphia Eagles suna gaba da Kansas City Chiefs a gasar Super Bowl na bana, inda suka doke zakarun gasar da ci 40 da 22.
Jama’a sun so ace Chiefs ne suka yi nasara a wasan, wadanda suka nufi filin wasan kwalon zari ka ruga da aka fi sani da American Football da fatar za su yi nasara a wannan karon su kasance zakarun wasar karo na uku a jere a wasan lig.
Sai dai Eagles ta hana Chiefs zura kwalo har sai kusan karshen zagaye na uku. A wannan lokacin kuwa, allon dake filin wasa na Ceasars Superdome a New Orleans na nuna cewa ‘yan wasan Pholadelphia sun samu maki 34.
An ayyana dan wasan Philadelphia Jalen Hurt a matsayin wanda ya fi burgew a wasan wanda ake kira da MVP.
Shugaba Donald Trump wanda yahallarci wasan, ya kasance shugaban Amurka mai ci na farko da ya taba yin hakan. Gabanin wasan, shugaban ya fitar da sanarwa mai cewa “wasan kwalon zari ka ruga shine wasan da ta fi farin jini a Amurka a bisa wani dalili mai kyau, yana inganta hadin kan kasa, yana hada iyalai, abokai da magoya bayan masu wasa wuri daya sannan yana dada karfafa al’ummomi.”
Ya kara da cewa, “wannan gasar da ake yi a duk shekara ta zarta banbance banbancen da ke tsakanin mu wanda yake bayyana dabi’un mu na kishin kasa, iyali, addini da ‘yancin mu, inda jami’an sojin kasar mu, jami’an tsaro da masu bada agajin gagawa suke karewa.”
An yi kiyasin cewa mutane sama da miliyan 120 ne za su kalli wasan da aka kashe dala miliyan $8 akan tallar wasan mai tsawon dakikai 30.
Kafin a fara wasan, an yi bukin bude taron da ya tuna da mutanen da suka mutu da wadanda suka ji rauni a mumunnan harin da aka kai wa mutane da motar akori kura a ranar sabuwar shekara a shahararren titin Bourbon a birnin New Orleans.