An saba ganin kananan yara ‘yan ‘kasa da shekaru 10 na ta gararamba kan tituna da tashoshin mota domin yin bara da kuma neman abin da zasu saka a bakinsu.
Hakan yasa kungiyar ta tara almajirai ta raba musu abinci da sutura da kuma Man shafawa.
A cewar shugaban NOVAD sheik Halliru Maraya, kulawa da almajirai zai taimaka da wajen rage al’amuran tashin hankali, domin kuwa rashin kulawa da su shine dalilin dake sa suna shiga yin abubuwan rashin zaman lafiya.
Shi kuma Rev John Joseph, cewa yayi abin da yara almajirai suke so shine a nuna musu ‘kauna da zumunci, a kuma mutunta su, domin kuwa Allah kadai ya barwa kansa sanin abin da yara zasu zama nan gaba.
Manyan malaman addinan Musulunci da Krista ne suka gudanar da jawaban janyo hankali ga almajiran da suka halarci taron.
Wasu daga cikin almajiran da suka samu cin moriyar wannan taro sun nuna jin dadinsu, tare da cewa tabbas hakan yasa sun ji a jikinsu ana kulawa da su.
Domin cikakken bayani saurari rahotan Isah Lawal Ikra.
Your browser doesn’t support HTML5