Kungiyar Miyetti Allah Taki Amincewa Da Sabon Shirin Gwamnati

Shugabannin Miyetti Allah

Kungiyar Fulani ta Miyetti Allah Kautal Hore tace shirin nan da gwamnatin tarayya ta bullo dashi na tsugunar da makiyaya waje guda da tayi wa lakabin Ruga, ya janyo rudani a tsakanin makiyaya a fadin Najeriya saboda rashin sanin alkibilar shirin.

Shugaban kungiyar ta kasa, Alhaji Bello Abdullahi Bodejo, yace sam basa goyon bayan shirin. Ya kara da cewa duk da goyon baya da suke baiwa gwamnati a shirye shiryenta masu kyau da take gudanarwa, batun shirin na ruga dai gwamnati bata tuntubesu ba.

Wasu manoma da gwamnatin tarayya tace ta bullo da shirin na ruga ne domin kawo karshen rikicin su da makiyaya su ma sun ce basu fahimci abubuwa da shirin ya kunsa ba don haka basu baiwa shirin goyon baya ba.

Mai magana da yawun matasan yankin Bokkos, a jihar Pilato, Macham Makut yace shirin na ruga zai janyo musu rashin zaman lafiya ne da abokan zaman su, makiyaya.

Farfesa Garba Hamidu Sharubutu dake kwararre a harkar kula da dabbobi yace tsugunadda dabbobin wuri guda zai kawo bunkasa a harkar kiwo da rage tashin tashina tsakanin manoma da makiyaya.

A halin da ake ciki dai gwamnatin tarayya ta dakatar da shirin zuwa nan gaba.

Wakiliyarmu a Filato Zainab Babaji ta shirya mana rahoto a kan haka:

Your browser doesn’t support HTML5

MIYETTI ALLAH TAKI AMINCEWA DA GWAMNATI