Tun farko dai mukaddashin kwamishinan ‘yan sanda DCP Usman Umar ya fara rasa ransa a sakamakon raunukan harbi da su ka samu kan sa a wajen zanga-zangar.
Shugaba Buhari ya gana da jagororin tsaro kan wannan akasi da ya faru duk da umurnin hana zanga-zanga a tsakiyar Abuja.
Babban sufeton ‘yan sanda Muhammad Adamu ya shaidawa manema labarai bayan ganawar cewa sun sanar da shugaba Buhari cewa kura ta lafa, inda shi kuma ya umurce shi su tabbatar da kare rayukan dukkan ‘yan Najeriya.
‘Yan Shi’an dai da su ka yi muzaharar a bayanan ‘yan sanda sun fi mutum 3000.
Kakakin ‘yan Shi’an dai na Abuja Muhammad Ibrahim Gamawa wanda yace sun rasa ran almajiran Elzakzaky kusan shirin, yace ba za su daina fitowa muzaharar ba sai an sake jagoran su.
Zuwa yammacin jiya komai ya koma daidai a tsakiyar Abuja, baicin motoci biyu na hukumar agajin gaggawa da suka kone kurmus a bigiren muzaharar.
Ga wakilinmu Isa Lawal Ikara da karin bayani a cikin wannan rahoto:
Facebook Forum