A taron gaggawar da shugabannin kungiyar na jihohi 19 suka gabatar a jihar Kano, matasan sunyi muhawar tare da nazari kan halin tsadar rayuwa da sauran kalubale da talakan Najeriya ke fuskanta musamman ma na Arewacin Najeriya.
Mallam Sani Mahmud Darma, shugaban kungiyar matasan ta Arewa Citizens Action for Change, cewa yayi ya kamata ace talakawan da suka dage kan wannan zabe ya zamanto akalla mutum yana iya cin abinci sau uku rana, ya kuma zamanto mutane sun sami saukin harkokin kasuwanci.
Sai dai matasan sun bayyana damuwa inda sukace dattawan Arewa sunyi shiru duk kuwa da radadin rayuwa da talaka ke fuskanta, wanda hakan yasa suka basu wa’adin makonni biyu da su daure su shirya wani gangamin taro a tsakaninsu don tattauna matsalolin dake faruwa a kasar.
Hakan dai na zuwa ne a dai dai lokacin da kungiyar Muryar Talaka ta matasa masu rubuce rubuce a shafukan sada zumunci ke ci gaba da yin Allah wa dai da matakin gwamnatin jihar Katsina, na kamawa tare da gurfanar da shugaban kungiyar na ‘kasa Bashir Madara a gaban Kuliya, bisa zarginsa da rubutun bata suna.
Saurari cikakken rahotan Mahmud Ibrahim Kwari.
Your browser doesn’t support HTML5