Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Zata Iya Sayar Da Kamfanonin Da Basu Da Amfani Ga Kasa


A dai dai lokacin da ake ta cece kuce a Najeriya tsakanin gwamnatin kasa da ‘yan kungiyar kwadago da kuma wani bangare na kwararru akan sha’anin tattalin arziki dangane da tasiri ko rashin tasirin Najeriya ta sayar da wasu kamfanoni domin samun kudin shiga.

Kwararre akan sha’anin tattalin arziki kuma tsohon babban darakta a bankin Unity da ke Najeriya mallam Ahmed Yusuf, ya bayar da wata shawara yake ganin cewa zata raba gardama tsakanin rukunan dake ja in ja a wata hira da yayi da manema labaru.

Mallam Yusuf dai yace yakamata a yi taka tsantsan da hattara akan matakin da za a dauka, a hirarsu da wakilin Muryar Amurka Umar Faruk, Yusuf yace lalle akwai muhimmancin a sayar da wasu hannayen jari ko kuma kamfanoni na gwamnati, amma kuma sai da hujjoji masu karfi.

Haka kuma Yusuf ya goyi bayan a sayar da kamfanoni ko wasu hukumomin gwamnati wadanda basu da amfani ga kasa, amma kada a sayar da wadanda suna da amfani kuma zasu iya gyaruwa har su kawowa gwamnati kudin shiga.

Saurari cikakken rahotan Umar Faruk daga Abuja.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:53 0:00

XS
SM
MD
LG