Jakadan Indiya a Najeriya Mr. Abhay Thakur, ya ce, akwai Indiyawa kimanin dubu 59 a Najeriya, hakanan akwai dubban ‘yan Najeriya a Indiya da ke gudanar da harkokin aiki, kasuwanci da sauran harkokin raya al’adu da tattalin arziki.
Mr.Thakur na zantawa da manema labaru ne a wajen taron baje kolin kayan saka, zaiyana da suturar mata “SARI” da kungiyar matan Indiya mazauna Abuja ta shirya.
Thakur ya ce, bukin ya faro ne daga Indiya da kuma ke da zummar raya al’adu da kara karfafa dangantakar tarihi tsakanin Najeriya da Indiya.
"Mu na alfahari da cewa akalla shugabannin Najeriya 3 sun samu gwanancewar aiki a cibiyoyin soja na 'yan gata a Indiya, Inji jakadan da ke yabawa Najeriya cewa ita ce mafi girman abokiyar huldar kasuwancin Indiya a Afirka.
Thakur ya ce, akwai shirin kulla dangantakar fina-finan Indiya “BOLLYWOOD” da na Najeriya “NOLLYWOOD”.
Aisha Yasmin na daga ‘yan kungiyar ta matan Indiya a Najeriya duk da mahaifin ta na da dangantaka da Najeriya, ta na mai cewa suturar SARI na nuna mutunci ne da al’adu na musamman matan aure a Indiya.
Shi kuma Mubarak Khan dan Najeriya ne da ke jin harshen Indiyanci da bai amince da caccakar Indiyawa da a ke ganin sun zubar da al’adun su, sun dau na yammacin duniya ba.
Taron ya samu halartar masu sana’o’in basira, masu daukar hoto da likitocin Indiya a Najeriya ciki da Mr.Sanjay K. Upadhyaya na asusun TULSI CHARAI FOUNDATION.
Ga cikakken rohoton daga wakilin muryar Amurka, Nasiru Adamu El-hikaya.
Your browser doesn’t support HTML5