Kungiyoyin 'yan Arewa a lagos sun koka game da rashin tsaro a jihohin
Arewa musanman yankin Zamfara da Sokoto da kuma Nigar. A taron manema labarai da wasu 'yan kungiyar ta Arewacin Najeriya suka gudanar, wasu sun yaba da matakan da aka dauka na tabbatar da tsaro, yayin da wasu kuma ke kushewa.
A kwanan nan ne wani kwamiti da jihar Zamfara da kafa, ya mika rahotan sa, inda aka ce an samu wasu sarakuna da iyayen kasa da kuma 'yan sanda da hannu dumu-dumu a harkokin rashin tsaro a jihar.
Wakilin Muryar Amurka Babangida Jibrin, yayi hira da sarkin kasuwar Alaba, Alhaji Umar Sokoto, da kuma wadandsu 'yan Arewa mazauna Legas domin jin tabakinsu da kuma ra'ayoyinsu game da wannan al'amari.
A saurari cikakken rahoto daga wakilin Muryar Amurka Babangida Jibrin.
Facebook Forum