Masana sha’anin noma sun tabbatar da cewa rashin amfani da iri mai inganci na daga cikin manyan dalilan da ke hana wa manoma cimma gaci a ‘yan shekarun nan a yankin Sahel, inda bayan shafe watanni sama da 3 na ayyukan gonaki a karshe su kan tashi a tutar babu saboda yadda akasarinsu ke amfani da irin gargajiya a wani lokacin da canjin yanayi ke haddasa dumamar yanayi da karancin ruwan sama.
Dalilin kenan da ya sa kungiyar masu noman iri ta yanke shawarar isar da irin zamani zuwa yankunan karkara wato kusa da talakka.
Wannan aiki da ke gudana da hadin gwiwar kwararru a fannin noma da sha’anin yanayi na hangen bunkasa noma a jamhuriyar Nijer ta yadda za a magance karancin cimakar da a ke fama da shi a kasar dake tsakiyar yankin Sahel, kamar yadda Sarauniyar Noma mai gandun ayi noma, Madame Nasser Aichatou ta bayyana mana.
Kungiyar na gargadin manoma su bada hadin kai ga wannan shiri domin riga kafin matsalolin da ke janyo fari a kasar da galibi aka fi noman hatsi da wake da dawa wadanda a gargajiyance ke bukatar dimbin ruwan sama da lokaci mai tsawo na damana .
Kimanin jihohi 5 da suka hada da Tilabery da Yamai da Dosso da Tahoua da Agadez ne zasu mori wannan tsari na bude shagunan irin zamani da kayan noman zamani, a albarkacin hadin gwiwar kungiyar manonan Iri da Projet ISSD Sahel.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5