Kungiyar Masu Kiwon Kaji Da Kwai Na Shirin Baje Koli

Muhammad Aminu Adamu, shine shugaban gonar Kaji da kwai ta Nana farms dake karamar hukumar Dawakin Tofa –Ya ce babban abinda ke haddasa tashin farashin kaji ko kwai a lokacin watan ramandana na da nasaba ne da yawan bukata da ake yi ta kaji da kwai a wannan lokaci, duba da yawan adadin jama’a da ke bukatarsu.

Malamin ya ce amma a mafi yawan lokuta mutane basa la’akari da hakan illa yawaitar dorawa masu harkar kwai da kaji laifin cewar ba sa saukaka wa jama’a da zarar watan ramadana ya kankama

Ya kara da cewa a yanzu yawancin wadanda basu cika amfani da kwai ba, sukan neme shi sakamakon sauyin cima da ake samu a watan ramadana domin farantawa iyali rai.

Haka kuma a matsayin su na kungiyar masu kiwon kaji, sun bude shaguna domin saukakawa al'umma baya ga wani tanadi na kai kwai filin baje koli domin saukar da farashin sa da kaji a wannan wata mai alfarma.

Daga karshe ya ce, a baya ana barinsu da tarin kwai sai sun tara da yawa masu saye su karyar musu da farashi ba tare da la’akari da irin kudaden da suka kashe kafin kaza ta kai ga yin kwan ba, hakan ne ma ya sa suka bude wasu shaguna domin gudan afkawa asara kamar yadda suka rika fuskanta a baya.

Your browser doesn’t support HTML5

Kungiyar Masu Kiwon Kaji Da Kwai Na Shirin Baje Koli Domin Saukakawa Al'umma