Kungiyar Manoman Shinkafa Ta Najeriya Ta Kaddamar Da Shirin  Bada Lamunin Kayan Noma Na Musamman Domin Karfafa Gwiwar Manoma

KUNGIYAR MANOMA

Yayin da damina ke kankama a sassan Najeriya, Kungiyar Manoman shinkafa, sarrafa ta da kuma kasuwancinta ta Najeriya ta kaddamar da Shirin ta na bada lamunin kayan noma na musamman domin karfafa gwiwar manoma.

A karkashin Shirin wadda aka kaddamar a karamar hukumar Garin Malam da ke makwaftaka da Kura cibiyar noman shinkafa ta jihar Kano, ana sa ran fiye da manoma shinkafa dubu goma sha biyu ne za su ci gajiyarsa, a wani mataki na habbaka noman shinkafa a wannan lardi.

KUNGIYAR MANOMA

Sarkin Noaman Adamawa Alhaji Mustafa Amadu da ke zaman shugaban kungiyar shine ya jagoranci kaddamar da Shirin a kauyen Dorawar Sallau na karamar hukumar Garin Malam. A cewarsa, “A kungiyance mu ka zauna da manoma da kamfanonin da ke samar da kayayyakin noma muka fahimci juna da su, yanzu gashi kayayyakin sun samu kuma mun kawo nan jihar Kano domin rarraba wa manomanmu lamani, inda za su fara biyan kashi 50% kuma bayan girbi su biya ragowar kashi 50% din”

KUNGIYAR MANOMA

Alhaji Nura Danjuma guda cikin manoman shinkafa a jihar Kano ya bayyana abin da manoma ke muradi dangane da harkokin su na noma. “Yace manoma na bukatar kayayyakin aikin noma da wuri kafin damina ta fadi, kamar iri da taki da sauran su”

Shi kuwa Malam Umar Bashir daga jihar Jigawa jan hankalin matasa ya yi game da mahimmancin noma ga ci gaban rayuwar, musamman la’akari da irin tsare-tsre da wasu kungiyoyin manoma ke bullo dasu.

Matakin kungiyar manoman shinkafa da sarrafa ta da kuma kasuwancin ta Najeriya na bada lamanin kayan noma ga ‘yayanta hadin gwiwa da kamfanoni masu zaman kansu, ya nuna yadda kungiyoyin manoma a Najeriya suka dawo daga rakiyar dakon kayayyakin bunkasa harkokin noma daga gwamnatin kasar.

Saurari rahoton Mahmud:

Your browser doesn’t support HTML5

Kungiyar Manoman Shinkafa Ta Najeriya Ta Kaddamar Da Shirin  Bada Lamanin Kayan Noma Na Musamman Domin Karfafa Gwiwar Manoma