Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

GHANA: Manoman Cocoa Na Fama Da Rashin Kudin Shiga Yayin Da Masu Sarrafa Alewar Cakulan Ke Samun Riba Sosai - Oxfam


Masu Sarrafa Alewar Cakulan
Masu Sarrafa Alewar Cakulan

Manyan masu samar da alewar cakulan a duniya suna samun riba mai yawa yayin da su kuma masu noman cocoa wadanda galibinsu ke fama da karancin kudaden shiga da kuma matsin talauci basa samun riba sosai, a cewar wani rahoto daga kungiyar agaji ta Oxfam.

An dai fidda rahoton ne gabanin ranar cinikayya ta duniya da za a yi ranar 13 ga watan Mayu.

Binciken ya mayar da hankali kan Ghana, kasa ta biyu a duniya da ta fi samar da cocoa. Kungiyar agajin ta ce kudaden da manoma a kasar ke samu sun ragu tun farkon barkewar cutar coronavirus a shekarar 2020.

"Binciken da kungiyar Oxfam ta yi kan manoman cocoa fiye da 400 da ke sama wa kamfanonin sarrafa alewar cakulan a fadin kasar Ghana, ya gano cewa kudaden shigar da manoman ke samu sun ragu da kashi 16 cikin 100 tun daga shekarar 2020, inda kudin shigar mata ya ragu da kusan kashi 22 cikin dari. Tara daga cikin manoma goma sun ce lamarin ya kara muni tun bayan barkewar cutar coronavirus, ”in ji rahoton.

Masu Sarrafa Alewar Cakulan
Masu Sarrafa Alewar Cakulan

Wadanda suka rubuta rahoton sun kara da cewa, kusan kashi 90 cikin 100 na manoman cocoa a Ghana ba sa samun kudin shiga da zasu yi harkokin gabansu, ma’ana ba za su iya samun isasshen abinci ko wasu kayan masarufi kamar tufafi, gidan zama ba, da kuma kula da lafiyarsu. Yawancin manoman cocoa 800,000 a kasar suna rayuwa ne a kan dala 2 a kowacce rana.”

Dalilai da dama a kasae da wadanda suka shafi kasashen duniya ne suka shafi kudin shigar manoman, a cewar Uwe Gneiting, mawallafin rahoton na Oxfam.

Masu Sarrafa Alewar Cakulan
Masu Sarrafa Alewar Cakulan

"Ba shakka annobar COVID ta kawo cikas sosai. Amma kuma yakin Ukraine da kalubalen tattalin arziki da ya haifar, tare da wasu dadaddun matsaloli, kamar tasirin sauyin yanayi da kuma tsofaffin gonaki da ake da su, sun taka rawa,” abinda Gneiting ya shaidawa Muryar Amurka kenan.

A lokaci guda kuma, kungiyar Oxfam ta ce ribar da manyan kamfanonin cakulan ke samu a duniya ta karu.

“Kamfanonin cakulan mafi girma huɗu na duniya, Hershey, Lindt & Sprüngli, Mondelēz da Nestlé, gaba dayansu sun sami ribar kusan dala biliyan 15 daga masana'antunsu tun farkon barkewar annobar COVID, karin kusan kashi 16 cikin 100 kenan tun daga 2020.

XS
SM
MD
LG