Kungiyar Liverpool A Shirye Take Ta Kai Labari Bana

Kocin Liverpool

Koci Kloop ya dau sabon alwashi ga kungiyarsa a kakar bana.

Tun bayan da Liverpool ta kammala gasar Firimiyar bana a mataki na biyu, da banbacin maki guda tsakaninta da Manchester City, wadda ta sake lashe kofin a bana.

Kocin Liverpool, Jurgen Kloop ya kalubalanci 'yan wasansa da su yi amfani da zafin rashin lashe kofin gasar firimiya, a matsayin wani kaimi da zai taimaka musu su lashe kofin zakarun Turai a bana.

Liverpool ta shafe shekaru 29 batare da ta lashe kofi lig na kasar Ingila ba.

Kocin Kloop yace don haka Liverpool za ta mayar da hankalinta ne kan lashe kofin gasar zakarun Turai, in da za ta kara da Tottenham a wasan karshe a birnin Madrid a ranar 1 ga watan Yuni 2019.

Sai dai kuma Liverpool itace kungiyar kwallon kafa da ta fi kowace kungiya a kasar Ingila lashe kofin zakarun turai UEFA Champions League inda ta dauka sau biyar.