Kungiyar Kwallon Matasan Najeriya Eaglet Ta Mayar Da Sansanin Ta Katsina

Golden Eaglets U-17

Kungiyar kwallon kafar matasan Najeriya masu kasa da shekaru 17 Golden Eaglet, sun mayar da sansanin su zuwa jihar Katsina, alokacin da suke ci gaba da shirye shiryen tunkarar gasar cin kofin duniya ta FIFA U-17, da za’a yi a kasar Chile.

Kamar yadda hukumar kwallon kafar Najeriya NFF ta fitar a shafin ta na yanar gizo, ‘yan wasa 35 da jami’ai 8 ne suka koma jihar Katsina dake Arewa maso Yammacin kasar. Shima koch Emmanuel Amuneke, ya dai nuna godiyarsa ga ma’aikatan Otel din Serob Legacy dake Abuja, da suka karramasu a daukacin zamanin su a birnin tarayya.

Inda yace, “muna gode kwarai da gaske ga karramawar da kukayi mana, amma yanzu dole ne koma Katsina domin ci gaba da shirye shiryen mu.”

Ya ci gaba da cewa da yardar Allah, zamu sake haduwa kuma muyi murnar abinda da Allah ya tanadar mana. Ranar Juma’a ne dai kungiyar matasan Eaglets tayi wasan kwawancen ta na karshe da Santos Academy, ta kuma samu nasarar lashe wasan da ci uku da babu.

An dai shirya yin wasannin gasar cin kofin duniyar tsakanin 17 ga watan Oktoba zuwa 8 ga watan Nuwamba.