Kungiyar Kwadagon Najeriya ta Kalubali Gwamnatin Tarayya kan Dakatar da Sanusi

Sanusi Lamido Sanusi

Tun da gwamnatin tarayya Najeriya tace ta dakatar da gwamnan babban bankin Najeriya Sanusi Lamido Sanusi ake kai ruwa rana.
Kurar da ta tashi tun lokacin da gwamnatin tarayya ta sanarda dakatar da gwamnan babban bankin Najeriya Sanusi Lamido Sanusi har yanzu bata lafa ba.

Kungiyar kwadagon Najeriya ta shiga jerin wadanda suka ki amincewa da abun da gwamnatin tarayya ta yi. Ta fitar da takardar sanarwa ga mutanen Najeriya da gwamnatui gaba daya cewa bata gamsu da yadda aka cire Sanusi Lamido Sanusi daga kujerarasa ba. Dalili kuwa shi ne gwamnan ya sanarda 'yan Najeriya cewa akwai almundahana a harakar aikin man fetur na kasar. Kungiyar tace idan ko da gaske gwamnatin Jonathan ta keyi cewa zata yaki cin hanci da rashawa da almundahana to kamaya ya yi ta jinjinawa Sanusi Lamido Sanusi amma sai gashi ta tsigeshi yayin da ya rage wata uku kacal ya kammala wa'adin aikinsa

Kungiyar kwadago tana ganin cire Sanusi da gwamnati ta yi bata bi ka'ida ba. Idan an duba dokar bakin da ma na kasa akwai yadda za'a zabi shugaban bakin da kuma yadda za'a dakatar da shi. A wannan karon gwamnati bata bi tsarin da aka shata ba. Cireshi ba shi ne maganin ba. Yanzu ma ba'a san adadin kudin da aka yi sama da fadi da su ba a harakar hada-hadar man fetur.

Kungiyar kwadago tace zata dauki mataki nan da dan gajeren lokaci a kan tabbatar da cewa 'yan majalisa sun yi abun da ya dace. Abun da ya dace kuwa shi ne su jinkirta tantance sunan wanda aka kawo ya maye gurbin Sanusi. Sai sun tabbatar da cewa nawa ne kudin talakawan Najeriya da suka bata. A kuma zakulo duk wadanda suka saci kudin kafin a yi maganar wani sauyi.

Gwamnati nada zabi. Ko ta mayarda Sanusi ya cika wa'adinsa kana ya tafi ko kuma kungiyar kwadago ta janye ma'akatanta daga kasar gaba daya. Kalubale ne babba a gaban majalisar kasa domin suna da haki su dauki mataki.

Your browser doesn’t support HTML5

Kungiyar Kwadagon Najeriya ta Kalubali Gwamnatin Tarayya kan Dakatar da Sanusi-3:17