A jawabinsa, Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya ce gwamnonin jihohin Najeriya za su sanya baki domin sasanta takaddamar da ke wakana tsakanin gwamnatin tarayya da kungiyar malaman Jami’o’i ta Najeriya ASUU, wadda ‘ya'yanta suka shafe watanni shida suna yajin aiki. Hakan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da kungiyar kwadagon Najeriya ta yi barazanar cewa, zata tsunduma yajin aiki na gargadi na kwana uku muddin gwamnati ta gaza sasantawa da kungiyar ta ASUU.
Kamar sauran jihohi, a yau kungiyar ta NLC ta jagoranci wata zanga zangar lumana wadda ta kunshi mambobin kungiyoyin dake karkashinta a matsayin kai agaji ga kungiyar Malaman Jami’o’i ta ASUU da sauran kungiyoyin bagaren ilimi dake yajin aiki game da takaddamar dake tsakaninsu da gwamnatin tarayya.
Zanga zangar ta hada da tattaki daga shataletalen mahadar titin Ahamadu Bello da na Murtala Mohammed zuwa gida gwamnatin Kano, inda shugabannnin kungiyar ta NLC bisa jagorancin shugabanta a Kano Comrade Kabiru Ado Minjibir suka mika wata wasika ga gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje, domin isar da ita ga ministan ilimin Najeriya Malam Adamu Adamu.
Yayin mika wasikar, shugaban kungiyar kwadagon Najeriya reshen jihar Kano, Comrade Kabiru Ado Minjibir, ya ce zanga zanagar lumanar da su ka yi, ita ce matakin farko na kai agaji tare da tallafi ga malaman Jami’o’in da kungiyarsu ta ASUU dangane da gwagwarmayar neman hakkinsu daga gwamnatin Najeriya.
“Muddin haka ba ta cimma ruwa ba, mtakinmu na ga ba shi ne yajin aikin gargadi na kwanaki uku da dukkanin mambobin kungiyar ta NLC za su shiga a fadin Najeriya, kana mataki na uku kuma shi ne yajin aiki na sai baba ta gani a fadin kasar, inji shugaban kungiyar kwadagon ta Najeriya reshen jihar Kano”
Gwamnan Kano wanda ya karbi kwafin wasikar ‘yan kwadagon zuwa Mininistan Ilimi Malam Adamu Adamu ya ce gwamnonin Najeriya za su shiga wannan magana domin ganin an sasanta, ta yadda dalibai zasu koma makaranta domin ci gaba da daukar darasi a aji.
Shugaban kungiyar ASUU reshen Jami’ar Bayero Kano, Comrade Haruna Musa yace sun yi maraba da wannan mataki na kungiyar NLC kuma hakan na nuna yadda magabantan kungiyar da-ma sauran ‘yan Najeriya suka damu da halin da gwamnatin Najeriya ta shiga da tsarin ilimin Jami’a a Kasar. Yace suna zuba ido domin ganin yadda makomar umarnin shugaba Muhammadu Buhari ga ministan ilimi kan cewa, lallai ministan ya warware wannan takaddama cikin makonni biyu.
Anasa bangaren, Comrade Abdulmalik Yunus mataimakin shugaban kungiyar manyan ma’aikatan Jami’ao’I da ba sa koyarwa yace suna da kwarin gwiwa cewa, matakin kungiyar ta NLC zai haifar da sakamakon mai alfanu.
Ga alama dai zanga zangar lumanar ta kungiyar NLC ta samu nasara da armashi la’akari da cewa, rassan kungiyar na jihohi tarayyar Najeriya 36 sun gudanar da ita cikin kwanciyar hankali.
Saurari cikakken rahoton Mahmud Kwari:
Your browser doesn’t support HTML5