Washington, D.C. —
A yau ne kungiyar kwadagon Nigeria NLC a takaice, ta fara gudanar da zanga-zanga a sassa daban-daban na kasar, domin nuna goyon baya ga yajin aikin da kungiyar malaman jami’a ta ASUU ta ke yi.
Malaman Jami’an dai sun shafe watanni kusan biyar suna yajin aiki, dan ganin Gwamnatin Tarayya ta cika musu alkawurran da ta yi musu na inganta tsarin karatun Jami’a, samar da kayan aiki da karin kudin alawus ga malaman.
A wata hirarsu da gidan Talabijin na Channels TV, shugaban kungiyar kwadagon Ayuba Wada, ya kare hakkinsu na yin zanga-zangar, sannan ya fadi cewa Kungiyar malaman Jami’ar tana karkashin kungiyar kwadagon, shi yasa suka fito domin mara masu baya.