Za a iya tunawa a makon da ya gabata ne aka samu rahoton bullar cutar shawara a jihar Bauchi daya kai ga rasa rayukan wasu mutane dasuka kai ziyara dajin shakatawa na Yankari dake jihar Bauchi, wanda a sanadiyar hakanne hukumar kula da lafiya ta majalisar dinkin duniya, da hadin gwiwar wasu hukumomin ayyukan lafiya suka hada karfi domin dakile cutar, dakuma hana bazuwarta.
Dokta Adamu Ibrahim Musa Ningi shi ne jami’in hukumar kula da lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya, ya yi karin haske kan shirin yakar cutar shawarar.
Cibiyar karewa daga kamuwa da cututtuka wato NCDC tayi bayanin irin rawar da za ta taka game da shirin yaki da cutar shawarar.
Dokta Isa Mai Dabino shi ne jami’in hukumar kula da lafiya a matakin farko a jihar Bauchi, ya ce akwai sauki kan batun cutar shawarar a yanzu.
Gwamnan jihar Bauchi Senata Bala Abdulkadir Muhammed Kauran Bauchi ya gode wa hukumomin kiwon lafiya da su ka kawo dauki ma jihar.
Ga cikakken rahoton daga wakilin Muryar Amurka Abdulwahab Muhammad.
Your browser doesn’t support HTML5