Wata babbar kungiyar kare hakkin bil'adama ta yi kira da a gudanar da bincike kan yiwuwar aikata laifukan yaki a kan sojojin Najeriya, da ta ke yaki da masu ikirarin jihadi, lamarin da ya janyo kona wasu kauyuka baki daya da kuma tilastawa mutane kauracewa matsugunansu.
Osai Ojigho, daraktan kungiyar Amnesty International a Najeriya ne ya yi kiran da a gudanar da wannan bincike. Ya ce ya kamata a dakatar da wandanda ake zarginsu, kuma hukumar tayi bincike domin a kaddamar da gaskiya a shari'a.
Kungiyoyin kare hakkin Bil'adama ta ce, ta yi hira da wasu mata da maza dama da aka kora daga gidajensu a yankin arewa maso gabashin kasar a farkon watan da ya gabata. Kungiyar Amnesty ta ce, zarginsu ya samu goyon bayan daga bayanan tauraron dan adam, wanda ya nuna cewa an kona kauyukan Bukarti da Ngariri da na Matiri. Binciken ya kuma nuna kone-kone a cikin wasu garuruwa na kusa, a cewar kungiyar kare hakkin.
Gwamnatin Najeriya ta sha musanta irin wadannan zarge-zargen na yiwuwar aikata laifukan yaki.