Kungiyar Kare Hakin Bil Adam Ta Zargi Rasha da Kashe Fararen Hula a Syria

Vladimir Putin shugaban kasar Rasha

Kungiyar nan da take rajin kare hakkin Bil'Adama ta kasa da kasa, Amnesty Intl. ta kara kan zarge zargen da ake yiwa Rasha a cikin wani sabon rahoto da ta bayyana jiya Laraba

Cikin sabon rahoton tana mai cewa a hare-haren da Rashar take kaiwa a Syria, ta kashe akalla mutane metan a lardunan Homs, da Idlib, da Aleppo.

Kungiyar mai kare hakkin Bil'Adama tace farmakin da Rashar take kaiwa da jiragen yaki, sun afkawa gidaje da kuma asibitoci, kuma binciken da ta gudanar ya nuna babu mayakan sakai, ko wasu sansanonin soja ko mayakan sakai kusa da inda ta kai hare haren.

Kamar yadda darektan kungiyar mai kula da shiyyoyin Gabas ta Tsakiya, da kuma Afirka ta yamma Phillip Luther yayi bayani, "irin wadannan hare hare suna iya zama laifuffukan yaki." Hakan nan, kungiyar ta Amnesty, tace tana da shaidar cewa Rasha tana amfani da albarusai da aka haramta wadanda ake kira "Cluster," da turanci, da bama-bamai wadanda basu da linzami.

Wani kakakin ma'aikatar tsaron Rasha, Igor Konashenkov, ya musanta zargin, yace rahoton bai kunshi wata sabuwar shaida ko wani abu sahihi ba, wadanda tuni kasar ta fito da su fili."

Haka nan Firayim Ministan Turkiyya Ahmet Dovutoglu, ranar Talata ya zafafa zargi da kasar take yiwa Rasha cewa, tana auna fararen hula da 'yan tawaye masu sassaucin ra'ayi a hare haren da take kaiwa.