A wurin taro, an karfafa guiwar masu ibada su yawaita karatun don neman kariya daga miyagun iri da su ka hada da masu satar mutane da 'yan boko haram.
Masu jawabi sun karfafa cewa yanda lamuran tsaro su ka addabi jama'a musamman arewa, zai yi kyau su yi amfani da karatun alkur'ani a watan mai alfarma don neman taimakon Allah.Da ya ke jagorantar taron shugaban JIBWIS Imam Abdullahi Bala Lau ya ce dama ce ga jama'a su rika sauraron karatun ko da ba su da haddar musamman a ramadan mai shigowa don samun taimakon Allah ga fitinar da ke addabar Najeriya.
Sauran manyan malaman da su ka hakarci taron sun hada da sautus sunnah Yakubu Musa Hassan Katsina, Sheikh Khalid Jos, Dr.Abdulsalam Babangwale da sauran su.
Saurari cikakken rahoton Nasiru Adamu El-hikaya daga Abuja:
Your browser doesn’t support HTML5