Tallafin da kungiyar ta baiwa zaurawan da marayu da gajiyayyu ya hada da dubban kudade da shaddodi da atamfofi.
Malam Salisu Abdullahi Umar shugaban kungiyar reshen jihar Oyo yace a gaskiya ba zai iya fada adadin mutanen da zasu samu tallafin ba. Amma an bayar da tallafi na akalla mutum 155 kawo yanzu. A bangaren zaurawa an samu goma sha biyar, marayu kuma dari da arba'in. An raba masu shadda da atamfofi da kudi kama daga dubu biyu biyu zuwa dubu biyar biyar.
Dangane da yadda suke samun kudaden da suke taimakawa mutane Malam Salisu yace ana samunsu ne ta wata hanya da shi shugaban kungiyar na kasa Sheikh Abdullahi Bala Lau ya shirya. Yayi wani kira ga duk 'yan kungiyar kuma ya mayar da ita doka cewa kowace jiha ta tafi ta kaddamar da asusun marayu. Yace a bi bangaren masu kudi su taimakawa addinin Musulunci domin a taimakawa marayu da zaurawa. Shirin yayi tasiri kamar yadda yayi bara.
Bara da suka fara a jihar Oyo sun samu nera miliyan daya da dari bakwai da sittin da dari biyar. Bana sun samu miliyan daya da dubu dari hudu da arba'in da hudu da dari hudu.
Sheikh Muhammed Sani Adarawa shugaban majalisar malaman jihar Neja yana daya daga cikin wadanda suka mika kyaututukan ga zaurawa da marayu da gajiyayyu. Ya kira sauran jihohi da suyi koyi da jihar Oyo kafin a zo kansu.
Wasu da suka samu kyaututukan sun bayyana jin dadinsu da kudi da shadda da aka basu.
Ga rahoton Hassan Umaru Tanbuwal.
Your browser doesn’t support HTML5