Manzo musamman na MDD yace kurdawa suna kare birnin Kobani daga mayakan Daular Islama ko ISIS wadanda suna gap da shiga garin. Staffan de Mistura ya fada jiya Talata cewa kurdawa suna anfani da kananan makamai yayin da mayakan Daular Islam ke anfani da manyan kayan yaki na zamani da tankuna.
De Mistura yace kurdawan suna yaki da jarumtaka amma yakamata kasashen duniya su taimaka masu domin kare kansu. Yace garuruwan da suka fada hannun Daular Islama sun sha kashin kare dangi da fyade da mugun tashin hankali.
Amurka tace hare-haren da take kaiwa akan mayakan Daular Islama kusa da Kobani sun yi tasiri.
Shugaban kasar Turkiya Recep Tayyip Erdogan yace harin bamabamai kawai basu isa ba sai an hada da sojojin kasa.To saidai kawo yanzu kasar Turkiyan bata nuna alama cewa ashirye take ta tura dakarunta su tsallaka cikin kasar Syria.