A ranar Asabar ne kungiyar IS ta ce ita ke da alhakin wani harin da aka kai kan sojojin Nijar a ranar Laraba, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar sojoji 30.
Kungiyar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da kamfanin dillancin labaran ta na Amaq ya fitar, kuma ta wallafa a kafar Telegram cewa, an kashe sojojin ne a wani harin kwantan bauna da aka kai kan ayarin motocin da sojojin ke ciki, kusa da garin Teguey da ke yankin Tillaberi a yammacin kasar ta Nijar.
Cikin wata sanarwa, a yammacin ranar alhamis, ma'aikatar tsaron kasar ta sanar cewa, an kashe sojoji 23 a harin, wasu su 17 kuma suka jikkata, yayin da aka yi nasarar kisan maharan 30.
Nijar dai na daya daga cikin kasashen yammacin Afirka da ke fama da hare-haren ‘yan ta’adda da ya bazu daga kasar Mali cikin shekaru 12 da suka gabata, lamarin da ya lakume rayukan dubban mutane tare da raba miliyoyin jama'a da muhallan su.
Bacin rai kan gazawar hukumomi wajen kare fararen hula, ya haifar da juyin mulkin da sojoji suka yi a Mali, Burkina Faso da Nijar tun shekara ta 2020.
Hukumomin mulkin sojan da suka kwace mulki sun yanke alaka da kawayen kasashen Yamma da ke taimaka wa kokarin sojojin cikin gida, inda suka fatattaki sojojin Faransa da sauran kasashen Turai, suka koma ga bangaren Rasha.
A makon da ya gabata ne dai gwamnatin Nijar ta soke yarjejeniyar soji da ta ba jami’an soji da ma’aikatan farar hula na Amurka damar shiga kasar ta.