Kungiyar Fulani Na So Gwamnatoci Su Dama Da Ardodi

Kungiyar matasan Fulani ta Jonde Jam, ta bukaci gwamnatoci da su bada muhimmanci ga tattaunawa da Ardodi wajen cimma manufofinsu da zai amfani makiyaya.

Shugaban kungiyar matasan Fulani ta Jonde Jam a Najeriya, Alhaji Saidu Maikano, ya ce, Ardodi sun fi kusa da al’umma, kuma ko a zamanin turawa sun bi ta hannun Ardodi ne don cimma manufar gwamnati.

Kwararre a harkar dabbobi a Najeriya, Farfesa Garba Sharubutu, ya ce, tsarin da gwamnatin tarayya ta bullo da shi na samar wa makiyaya saukin kiwo, ta yi ne don magance matsaloli.

Ga cikakken rahoton wakiliyar Muryar Amurka Zainab Babaji daga Jos.

Your browser doesn’t support HTML5

Kungiyar Fulani Ta Jonde Jam Tana so Gwamnatoci Su Basa Fifiko