Kungiyar Fafutikar Tabbatar da Da'a Ta Kai Shugaban Amurka Trump Kara

Shugaban Amurka Donald Trump

Kwanaki uku kawai da fara mulki, Shugaban Amurka Donald Trump na fuskantar kalubalen shari'a na farko a gwamnatinsa.

Wata kungiyar saka ido mai suna 'Yan Kasa Masu Fafatukar Tabbatar da Da'a da Gaskiya a Washington, ko CREW a takaice, ta gabatar da kara jiya Litini a birnin New York, ta na mai tuhumar cewa jerin kamfanonin da Shugaban kasar ya mallaka, sun sa ya samu kansa a yanayi na saba ma wani bangaren kundin tsarin mulkin kasa.

Nan da nan dai Trump ya yi watsi da karar, ya na mai cewa, wannan karar, a ta bakinsa, "kwata-kwata ba ta bisa hujja."

Su na kafa hujjarsu ce kan abin da ake kira 'tanajin doka kan biyan kudi' na kundin tsarin mulkin kasa, wanda ya tanaji cewa kar manyan kasa ko gwamnatoci su biya kudi ko su yi kyauta ga Shugaban kasa ba tare da yaddar Majalisar Tarayya ba.'

A cewar jaridar New York Times, wadda ita ce ta fara buga labarin ranar Lahadi, karar ba ta bukatar cin tara, ta na bukatar Shugaban kasa ne ya daina amsar duk wani kudin da wata kasar waje ta biya shi.

Kungiyar ta CREW ta ce Trump ya ki ya sayar da kamfanoninsa kwata-kwata, "A halin yanzu ya na ansar kudi da kuma alfarma daga gwamnatocin kasashen waje, ta wajen biyan kudi da masu shiga gidajensa na haya da otel oteldinsa da kuma masu gudanar da wasu harkoki a otal-otal din ke yi da kuma sauran harkoki a kasashen waje.'