Kungiyar ECOWAS Tace Zata Yaki Cin Hanci da Rashawa

Shugabannin kasashen ECOWAS

Shekaru 41 ke nan da kafa kungiyar ECOWAS ko CEDEAO da zummar habaka tattalin arzikin kasashen na yammacin Afirka da samarda sukunin zirga zirga tsakanin al'ummomin kasashen ba tare da wata tsagwama ba.

To saidai kungiyar tace a yau, bayan shekaru arba'in da daya da kafata, lamarin ba haka yake ba idan aka yi la'akari da yadda ake karban na goro a hannun matafiya tsakanin kasa da kasa.

Dalili ke nan da babban kwamishananta yace dole kungiyar ta sake lale idan har tana son cimma muradunta. Kwamishanan ya yi wannan furunci ne yayinda yake ziyara a birnin Yamai fadar gwamnatin Nijar.

Kungiyoyin kare hakkin dan Adam da masu rajin kare dimokradiya, tuni suka fara tofa albarkacin bakinsu akan sabuwar albiklar da ECOWAS din ke shirin dosa.

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya a taron ECOWAS

Abdu Alhaji Idi jagoran wata kungiya yace idan har da gaske jami'in ECOWAS din yake yi, yace mutane suna son su gani a kasa. Idan har mutum zai iya tashi daga Yamai ya tsara kasashen yammcin Afirka har ya kai Mali ba'a tambayeshi kudi ba, wato tafiya daga wannan kasa zuwa waccan cikin walwala ba tare da bada na goro ba akan iyakoki, shi ne talakawa ke son gani.

Alhaji Idi yace kungiyar yanzu ba ta 'yan kasa ba ce, ta shugabannin kasashen ne domin suke balaguro daga wannan kasa zuwa waccen su yi taro, su sha shayi da lemu kana su watse. Amma talaka koina zashi yana cikin matsi na mahukunta akan hanya

Kungiyar ta dorawa Shugaba Buhari na Najeriya da Alassane Ouattara na Ivory Coast da John Dramani Mahama na Ghana da Issoufou Muhammadou na Nijar alhakin gaggauta binciko hanyoyin da zasu bada damar kirkiro da kudade na bai daya a yakin ECOWAS.

Wani masanin tattalin arziki Dr. Soli Abdullahi yace kirkiro da kudin bai daya da kasashen ECOWAS zasu yi anfani dashi ya yi daidai. Yace yanzu idan mutum ya bar Nijar zashi kowace kasa cikin yammacin Afirka dole ne sai ya canza kudin Nijar zuwa na kasar da zashi.

Masu kula da alamuran yau da kullum na ganin yunkurin da ECOWAS ta yi yanzu na kawo canji a lamuranta ba zai rasa nasaba da daratsin da ta koya daga abun da masu jefa kuri'a suka yi a Birtania ba inda da karfin kuri'unsu suka fitar da kasar daga kungiyar Turai

Ga karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Kungiyar ECOWAS Tace Zata Yaki Cin Hanci da Rashawa - 3' 04"