A Najeriya , yayin da ake kokarin tada komadar makarantu da rikicin Boko Haram ya shafa a jihohin arewa maso gabas, yanzu haka Kungiyar Dillalan Man Fetur Masu Zaman Kansu wato IPMAN ta kaddamar da wata gidauniyar tallafawa Makarantun firamare da kayyakin karatu da kuma na kiwon lafiya.
Daman dai bincike ya nuna cewa a jihohin arewa maso gabas akwai makarantu da dama dake cikin ha’ula’I, masu matsananciyar bukatar tallafi a yanzu, duk da ikrarin da gwamnatocin jihohin ke yin a cewa suna nasu kokari.
Kayan tallafin da suka hada da magunguna, kujeru, wuraren zuba shara, da ma randunan ruwa na zamani, na zuwa ne yayin da ake kokarin tada komadar makarantu da rikicin Boko Haram ya shafa a jihohin arewa maso gabas.
A jihar Adamawa, daya daga cikin jihohin da rikicin na Boko Haram ya shafa, hadakar kungiyar dillalan man fetur ta ce daukan wannan mataki na cikin kokarin da kungiyar ta soma don hada karfi da karfe don kawo cigaban al’umma.
Tun farko da yake jawabi, mai martaba Lamidon Adamawa, Dr Muhammadu Barkindo Aliyu Musdafa, wanda Dan Amar Adamawa kuma Hakimin Jimeta, Alhaji Muhammad Baba Paris ya wakilce shi, yace lokaci yayi da za’a daina dogaro da gwamnati akan kowane lamari.
Su ma malaman makarantun da aka baiwa agajin sun yaba ainun da wannan tallafin da suka samu.
Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5