Kungiyar City Oilers Ba Zata Mika Kai Bori Ya Hau Ba Duk Da Cewar An Yi Galaba Akanta Da Ci 0-3 - Opong

City Oilers vs. Al Ahly Ly

Wannan ne karo na 3 da zakarun kasar Ugandan suka yi rashin nasara a matakin rukuni inda suke da kwantan wasa 3. Saidai mai tsaron bayan Oilers, Robinson Opong ya dage akan cewar ba zasu mika kai ba.

WASHINGTON DC - City Oilers ce kungiyar kwallon kwando daya tilo da tayi rashin nasara a gasar Nile Conference ta bana inda Al-Ahly tayi galaba akanta da ci 79 da 68 a Litinin din data gabata.

“Wajibi mu cigaba da nuna kwarin gwiwa, “ a cewar Opong wanda ya kare gasar da samun nasarar jefa kwallaye 11 a raga da rashin nasara a 8. Abinda kungiyar oilers ke bukatar yi, a cewar opong shine “maida hankali akan wasa na gaba, tare da kallan fina-finan wasanni da kokarin inganta kwazonmu cikin dan kankanin lokaci.

Koda aka tambaye shi game da karin kwazon daya kamata Oilers su yi, sai opong ya bada amsa da cewar, “bamu sanya kwazon daya dace ba. Dole mu inganta akan hakan. “Al-Ahly ta samu ci gaba da ci 2 da 1 gabanin ranar hutun gasar ta Nile Conference na ranar Talata 23 ga watan Afrilun da muke ciki.

Dukkanin kungiyoyin 4 zasu cigaba da fafata gasar a ranar Laraba inda City Oilers zasu barje gumi da masu masaukin baki Al-Ahly a yayin da Bangui Sporting Club itama zata kece raini da Al-Ahly