Gwamnonin Adamawa, Borno da Yobe sun koka da abun da suka kira sakaci da ake yi wajen yaki da 'yan Boko Haram a yankinsu.
Bayan taron gwamnonin mataimakin gwamnan jihar Borno yace kawo yanzu sun yi asarar kananan hukumomi goma sha uku da yanzu suna hannun 'yan Boko Haram din. A jihar Adamawa kuma kananan hukumomi hudu ne ke hannun 'yan kungiyar. Wadannan kuwa sun hada da Madagali, Michika, Mubi ta Arewa da kuma Mubi ta Kudu.
Yace muddin ba'a dauki matakan da suka dace ba 'yan Boko Haram zasu kwace jihohin uku kacokan ko kuma duk ilahirin arewa maso gabashin Najeriya.
Mataimakin gwamnan Borno yace yau basu iya zuwa kananan hukumomi goma sha daya ba domin suna hannun 'yan kungiyar. Tafiya daga Maiduguri zuwa Biu a da awa daya da rabi ne ko awa biyu amma yanzu sai an yi awa takwas ko goma. Masu zuwa Askira Uba maimakon awa biyu daga Maiduguri yanzu sai sun bi ta Yola kana su kwana a hanya kafin su kai inda zasu. Haka lamarin yake tun cikin watanni uku da suka gabata. Suna cikin wani mawuyacin hali da ya kamata gwamnatin tarayya ta sake dubawa.
Tunda rikicin Boko Haram ya hada da kasashe hudu, wato Najeriya, Kamaru, Chadi da Niger kamata yayi a nemi taimakon kasa da kasa domin a shawo kan lamarin. Idan an kira kasashe kamar su Iran da Iraki ko jiragen yaki hamsin suka taimaka dasu nan da wata daya rikicin zai kawo karshe.
Mataimakin gwamnan Borno yace tun can farko shi bai yadda batun sulhu tsakanin gwamnatin Najeriya da 'yan kungiyar Boko Haram gaskiya ne ba. Da gaskiya ne lokacin da aka ce za'a saki 'yan matan Chibok da sun fito. Maganar ta banza ce domin shi shugaban Boko Haram din yace ya aurar da 'yan matan kuma tuni sun tafi gadajen mazajensu.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5