Wannan harin shi ne na baya bayan nan cewa 'yan Boko Haram sun kaiwa Fulani hari tare da kore shanun Fulanin da yara kanana biyar.
To saida hudu daga cikin yaran da shekarunsu bai wuce takwas zuwa goma ba sun samu sun sulale daga hannun 'yan Boko Haram din. Yaran sun shaida cewa an kaisu cikin wani kurmi ne cikin daji kuma ba zasu iya gane inda wurin yake ba. Yayinda suka sulale na biyar din yana barci
Alhaji Ahmadu Wusa shi ne shugaban kungiyar Miyetti Allah ta Najeriya reshen arewa maso gabas ya tabbatar da kashe Fulanin a kauyen Alau cikin karamar hukumar Konduga akan hanya ta zuwa cikin dajin Sambisa. Yace yankin Alau din ne suke samun ruwa saboda sauran wuraren babu ruwa babu ciyawa.
Cikin Fulanin daya da kwananshi bai kare ba ya gudu shi ne ya kai labarin abun da ya faru da sauran. Yace abun da zasu taimakawa gwamnati shi ne labarun siri kuma watakila dalilin da ya sa 'yan Boko Harem ke kashe Fulani ke nan.
Ko makonni biyu da suka wuce 'yan Boko Haram sun kashe Fulani sittin wajen Pulka. Sun kwashe shanu sama da budu tumaki kuma sun kai dubu biyu. Sojoji sun taimaka an samu shanu sama da 140 amma suna rokon sojoji su kara taimaka masu a gano sauran.
Alhaji Ali Muhammad babban ubangidan kungiyar Miyetti Allah yace har yanzu basu ga wani tallafi ba walau daga gwamnatin tarayya ko ta jiha game da bala'in dake samunsu daga kungiyar Boko Haram..
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5