Kungiyar AU ta Nada Wakilai 3 Don Su Taimaka Wajen Warware Rikicin Habasha

Shugaban Afrika ta kudu Cyril Ramaphosa

Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya ya yaba da kokarin AU na nada wakilan da zasu tamaika wajen sasanta rikicin kasar Habasha.

Kungiyar hadin kan Afrika ta AU ta nada manyan wakilai 3 don shiga tsakani wajen zaman shawarwarin warware rikicin sojan da ake yi a yankin Tigray da ke Habasha.

Shugaban kungiyar ta AU shugaba Cyril Ramaphosa na Afrika ta kudu ya sanar da shugabar Habasha Sahle-work Zewde ranar Juma’a 20 ga watan Nuwamba cewa ya nada tsohon shugaban Mozambique Joaquim Chissano, da tsohuwar shugabar Liberia Ellen Johnson-Sirleaf, da tsohon shugaban Afrika ta kudu Kgalema Motlanthe a matsayin wakilan AU na musamman da aka dorawa alhakin taimakawa a zaman shawarwari tsakanin bangarorin biyu don kawo karshen rikicin kasar Habasha.

Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya fitar da wata sanarwa jiya Juma’a da maraice, yana mai na’am da nadin ya kuma yabawa Ramaphosa akan wannan kokarin tare da mika tayin cikakken goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya wajen tabbatar da zaman lafiya, kwanciyar hankali da ci gaban kasar Habasha.