A wannan sabon rahoto da ta fitar, kungiyar ta Amnesty ta ce, wasu matakai da shugabannin suka dauka a kasashen Masar da Philippines da Venezuela da China da Rasha da kuma Amurka, sun take hakkokin bil adaman miliyoyin jama’a.
Rahoton ya ce, dangane da kasar Philippines, shugaban kasar Rodrigo Deterte, ya fito karara ya yi kira ga mutane da su kashe wadanda ake zargin suna dillancin muggan kwayoyi.
Rahoton kuma ya caccaki shugaban Amurka, Donald Trump, kan matakan da yake dauka na shige da fice a kasar, da tauye walwalar ‘yan jarida da kuma irin tarihin da ya kafawa kansa, dangane da hakkokin mata.
Muryar Amurka ta nemi jin ta bakin Fadar shugaban kasa ta White House, kan wannan rahoto na kungiyar ta Amnesty, amma haka ba ta cimma ruwa ba.