A can kasar Somaliya , jiya Lahadi aka harbe wata 'yar jarida mai suna Sagal Salad Osman a birnin Mogadishu, wadda take yiwa gidan rediyon talibijan na kasar.
WASHINGTON DC —
Babban sakataren kungiyar 'yan jarida ta kasar Somaliya Mohammed Ibrahim Moalimu ya fadawa Muryar Amurka cewa wasu 'yanbindiga da ba'a san ko su wanene ba suka harbe Sagal a gundumar Hodan a lokacin da take barin wata jami'a.
Yace nan da na yan bindigan suka arce daga wurin.
Sagal Osman itace 'yar jarida mace ta biyu da aka kashe a kasar Somaliya cikin watanni shida da suka shige.
A watan Disamban shekara ta dubu biyu da goma sha biyar aka kashe wata 'yar jarida mai suna Hindi Hajj Muhammad a sakamakon wani hari da aka kai da wani bam da aka boye cikin wata mota.
Kungiyar Al Shabab tayi ikirarin cewa ita ke da alhakin kai harin