Kungiyar al-Shabab Na Shirin Kai Hari a Uganda

Shugaban Uganda Yoweri Museveni

'yansandan Uganda sun ce sun samu sahihin labari cewa kungiyar al-Shabab na shirin kai hari a Kampala babban birnin Uganda

‘Yan sanda a Uganda sun ce sun sami wani “sahihin labari” cewa, kungiyar mayakan Somaliya al-Shabab tana shirin kai hari a Kampala babban birnin kasar.

Gargadin ya biyo bayan irin wannan sanarwar da ofishin jakadancin Amurka a Kampala ya bayar tun farko.

Sanarwar ‘yan sandan tace yana yiwuwa kungiyar al-Shabab ta kai hari kan wuraren da ake samun hada hadar jama’a kamar otel otel da kasuwannin zamani da sauran kasuwanni da wuraren shakatawar jama’a. An shawarci al’aumma, da su sa ido matuka, kan duk wadansu take take, ko wani abinda suke shakku a kai.

Gwamnatin kasar Uganda ta fada ta hanyar sadarwar twitter cewa, an dauki kwararan matakan ganin an dakile yunkurin kai hare haren.

Ranar Laraba ofishin jakadancin Amurka yace, ya soke wadansu kananan ayyukan da aka yi shirin gudanarwa a otel otel dake kasar bisa dalilan tsaro.