Tawagar kasar Amurka zuwa kasar Sudan ta Kudu ta bukaci bangarorin biyu masu fada da juna da su sake darewa kan teburin sulhu.
Wannan shawara dai tazo ne kwana daya bayan da Majalisar Dinkin Duniya tayi gargadincewa duk wanda ke kawo wa tsarin zaman lafiya barazana to zata kakaba masa takunkunmi.
Jakada Donald Booth ya fada wa taron manema labarai a babban birnin kasarna Juba cewa hanyar samar da zaman lafiya da lumana shine ta tattaunawa tsakanin bangarorin biyu.
Booth ya jaddada cewa kudirin kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya shine tankunkumin ba zai kyale wasu daidaikun mutane ba na kasar masu kawo wazaman lafiya cikas.
Yace duka bangarorin suna anfani da dodorido domin shuka tsoro a zukatan wasu yan kasan
Ita dai kasar Sudan Ta Kudu ta samu damar zamowa kasa ce mai yancin cin gashin kanta daga tsohuwar kasar Sudan ta arewa a shekarar 2011 tare da goyon bayan Amurka.
Amma kwaran kuma sai yaki ya barke tsakanin su a cikin watan disembar shekarar 2013 bayan da shugaban kasar Salva Kirr ya zargi mataimakinsa Riek Machar da kokarin yi masa juyin mulki.
Yanzu haka dai fada a wannan kasar ta Arewacin Africa yayi musabbabin kashe dubban mutane kana ya raba sama da miliyan 2 da muhallansu. Yanzu kasashen duniya suna ta kokarin ganin an samu zaman lafiya a wannan kasar amma shugaba Salva Kirr da mataimakin nasa Marchar sun kasa su cimma matsaya akan rabon iko idan an zo kafa gwwamnatin hadin kan kasa