Kungiyar Al-Shabab ce ta horas da Boko Haram - Shugaban Somalia

Shugaban Najeriya Muhammad Buhari da na Somalia Sheik Hassan Mahmud

A taron kasa da kasa da aka yi akan harkokin tsaro a kasar Jamus Shugaban kasar Somalia ya fada jiya Lahadi cewa kungiyar al-Shabab ta kasarsa ce ta horas da 'yan Boko Haram

Wani masanin harkokin tsaro Dr Abdullahi Wase yace ba za'a iya musanta furucin na shugaban Somalia ba.

Shi dai shugaban na Somalia Sheik Hassan Mahmud ya fada jiya Lahadi a wurin taron kasa da kasa akan harkokin tsaro da ake yi a kasar Jamus cewa 'yan ta'adan kasarsa ne suka horas da na kasar Najeriya.

To saidai ko hakan ya faru daga shekaru biyu ko uku suka wakana saboda lokacin da kungiyar Boko Haram ta bullo a shekarar 2009 bata anfani da bamabamai irin na al-Shabab. Abu na biyu da za'a lura dashi shi ne Somalia bata da iyaka da Najeriya. Najeriya na yammacin Afirka ita kuma Somalia tana gabashi. Abu na uku baindigogin da suke anfani dasu sun banbanta. Amma tana yiwuwa shi shugaban ya samu wasu rahotanni na musamman.

Ga karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Kungiyar Al-Shabab ce ta horas da Boko Haram - Shugaban Somalia - 10' 01"