Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jirgin Sama Mai Sarafa Kansu Ya Halaka 'Yan Kungiyar Al-Shabab a Wani Hari


Some al-Shabab leaders
Some al-Shabab leaders

Wani harin sama na jirgi mara matuki da ake zargi na Amurka ne, ya kaikaici wata tungar mayakan Al Shabab a Somaliya.

Har yanzu babu cikakkun bayanai kan wannan hari da aka kai a daren Litinin din da ta gabata, amma jami’an yankin sun ce, harin ya halaka mayakan kungiyar da dama, ana kuma tsammanin ya rutsa har da wani babban kwamandan kungiyar.

Wasu rahotanni sun ce harin ya kaikaici wani jerin gwanon motocin kungiyar ta Al- shababa ne, yayin da wasu rahotanni ke cewa sansanin ‘yan kungiyar harin ya shafa, wanda ke yankin Shabelle.

Ya zuwa yanzu dakarun Amurka ba su ba da tabbacin kai wannan hari ba, amma sansanonin kungiyar ta Al shabab, wurare ne da Amurka ke yawan kai hare-hare da jirage mara matuka.

Irin wadannan hare-hare da ake kaiwa da hadin gwiwar dakarun Afrika, sun jima suna kassara ayyukan kungiyar ta Al shabab, wacce ke yunkurin kifar da gwamnatin kasar.

XS
SM
MD
LG