Mutane da dama daga Jihohi takwas a Jamhuriyar Nijar sun halarci taron shekara shekara na Kungiyar Ahmadiyya wacce ke da asali daga kasar Pakistan a karkashin jagorancin gwamnan jahar Tahoua Malam Musa Abdurahamane wanda ya wakilci bangaran gwamnatin kasar.
Wannan kungiya ta Ahmadiya ta shigo cikin Jamhuriyar Nijar a shekara 2000, inda ta fara gina masallatai, rijiyoyi, fanfuna burtsatsai, makarantu da kuma cibyoyin kungiyar a cikin birane da kauyuka.
Taken taron wannan shekara na kasa shine “Neman Ilimi na addini dana zamani wajibi ne ga dukkan musulmi.
Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta dau matakan tsaro a wurin taron, inda aka saka jami’an ‘yan sanda na musamman wasu masu kayan sarki da kuma wasu cikn farin kaya domin tabbatar da tsaro a gurin, saboda irin abubuwan marasa dadin ji da suke faruwa a guraran taro irin wannan a kasashen ketare.
Saurari cikakken rahoton Haruna Mamane Bako:
Your browser doesn’t support HTML5