A wata hira da yayi da Muryar Amurka, kakakin kungiyar kwadago ULC kwmred Nasir Kabir, ya zargi shugaban Najeriya da sauran majagorantan kasar da cewa, saboda su bukatunsu suna tafiya basu ma san abunda sauran 'yan kasar suke ciki ba.
Kakakin kungiyar ya fadawa wakilin Sashen Hausa na Muriyar Amurka Hassan Maina Kaina cewa, sun tashi baram-baram a tattaunawar da suka yi da ministan kwadago Chris Ngige, wanda ya bukaci 'yan kwadagon da su janye batun shiga yajin aiki, saboda gwamnonin jihohi da dama sun ce ba za su iya biyan sabon albashin mafi karanci ba.
Ana sa banagaren Minista Ngige yace, gwamnati tana da kyakkyawar manufa ga ma'aikata, domin ko a yanzu suna dakon isowar wasu kwararru da za'a ci gaba da shawarwari kan wannan batu.
Amma kakakin kungiyar yace sun shaidawa ministan cewa an wuce wannan mataki, abu na gaba shine aiwatar da sabon tsarin albashin ba wai wani sabon jan kafa ba.
Ga rahoton Hassan Maina Kaina.
Your browser doesn’t support HTML5